Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya WAS ya bayar da sanarwar cewa, sarkin masarautar kasar ya sauke Muhammad Bin Naif ne daga dukkanin mukaman da yake rike da su, da suka hada da yarima mai jiran gado, ministan harkokin cikin gida da kuma mataimakin Fira minista.
Yayin da Muhammad Bin Salman dan sarkin kasar ta Saudiyya dan shekaru 31 da haihuwa, zai maye gurbinsa a matsayin yarima mai jiran gado kuma mataimakin fira minista, a lokaci guda kuma Muhamamd Bin Salman shi ne ministan tsaro, kuma shugaban babban kamfanin mai da isakar gas na kasa (ARAMCO).